Hausa translation of the meaning Page No 578

Quran in Hausa Language - Page no 578 578

Suratul Al-Qiyamah from 20 to 5


20. A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan ( duniya ) ne.
21. Kunã barin ta ƙarshen ( Lãhira ) .
22. Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
23. Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
24. Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
25. Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
26. A'aha! Iadan ( rai ) ya kai ga karankarmai.
27. kuma aka ce: « Wãne ne mai tawada? »
28. Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
29. Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
30. Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa ( 1 ) take.
31. To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
32. Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
33. Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
34. Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
35. Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
36. Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga ( wãto bãbu nufin kõme game da shi ) ?
37. Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa ( a cikin mahaifa )
38. Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
39. Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
40. Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu? ( 2 )
Sũratul Insãn
Tana karantar da asalin mutum da yadda zai ƙare, ko ya dõge idan yã bauta wa Allah.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata.
2. Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,
3. Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci.
4. Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr.
5. Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne.
( 1 ) Ranar kora mutane, kamar ana gargaɗa tumãki, zuwa ga tsayi a gaba ga Allah, dõmin hisabi.
( 2 ) Ana son mai karãtu a nan ya ce: a ɓoye