Hausa translation of the meaning Page No 579

Quran in Hausa Language - Page no 579 579

Suratul Al-Dahr from 6 to 25


6. Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa.
7. Suna cikãwa da alwãshin ( da suka bãkanta ) , kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne.
8. Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme.
9. ( Suna cẽwa ) : « Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya. »
10. « Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa. »
11. Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki,
12. Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini.
13. Sunã mãsu zaman ginciri, ( 1 ) a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura.
14. Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa.
15. Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau.
16. Ƙarau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta.
17. Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne.
18. Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.
19. Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa.
20. Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba.
21. Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar ( ciki ) .
22. ( A ce musu ) « Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa. »
23. Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa.
24. Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci.
25. Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice.
( 1 ) Kishingiɗa.