Hausa translation of the meaning Page No 586

Quran in Hausa Language - Page no 586 586

Suratul Al-Takwir from 1 to 29


Sũratut Takwĩr
Tana karantar da Tãshin ƙiyãma gaskiya ne, kuma Alƙur’ãni gaskiya ne, daga Allah yake, bãbu ragi bãbu ƙãri, yã taho ta hannun aminci, daga Allah zuwa ga Annabi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Idan rãna aka shafe haskenta
2. Kuma idan taurãri suka gurɓãce ( wani ya shiga a cikin wani ) .
3. Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
4. Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna ( 1 ) aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
5. Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
6. Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
7. Kuma idan rãyuka aka haɗa ( 2 ) su da jikunkunansu.
8. Kuma idan wadda aka turbuɗe ( 3 ) ta da rai aka tambaye ta.
9. « Sabõda wane laifi ne aka kashe ta? »
10. Idan takardun ayyuka aka wãtsa su ( ga mãsu su ) .
11. Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
12. Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
13. Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
14. Rai ya san abin da ya halartar ( a rãnar nan ) .
15. To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ( 4 ) ba.
16. Mãsu gudu suna ɓũya.
17. Da dare idan ya bãyar da bãya.
18. Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
19. Lalle ne shi ( Alƙur'ãni ) haƙƙan, maganar wani manzon ( Allah ) ne mai girma ga Allah.
20. Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
21. Wanda ake yi wa ɗã'a ( wato shugaban malã'iku ) ne a can, amintacce.
22. Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
23. Kuma lalle ne, yã gan shi ( 5 ) a cikin sararin sama mabayyani.
24. Kuma shi, ga gaibi ( 6 ) bã mai rowa ba ne.
25. Kuma shi ( Alƙur'ani ) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
26. Shin, a inã zã ku tafi?
27. Lalle ne shi ( Alƙur'ãni ) , bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
28. Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
29. Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.
( 1 ) Rãƙuma mãsu ciki ɗanwata gõma.
( 2 ) Ko kuma, aka haɗa kõwane mutum da irin mutãnensa a Aljanna ko a wuta.
( 3 ) A cikin zãmanin jahiliyya Lãrabãwa bã su son a haifa musu 'ya'ya mãta dõmin haka har sukan turbuɗe 'ya'yansu dõmin kada su yi abin kunya ko kuma su talauce wajen yi musu aure.
( 4 ) Masu tafiya suna kõmawa bãya.
( 5 ) Annabi ya ga Mala'ika Jibirilu ya san shi. Sabõda haka wani aljani bã zai yi kama da shi ba balle ya kãwo masa ƙarya.
( 6 ) Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cẽwa daga Allah yage, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne.