Hausa translation of the meaning Page No 587

Quran in Hausa Language - Page no 587 587

Suratul Al-Infitar from 1 to 6


Sũratul Infiɗãr
Tana karantar da gaskiyar Tashin Ƙiyãma, kuma ayyukan mutum na dũniya ana tsare da su dõmin hisãbi da sakamako. Akwai malã’iku matsara na musumman.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Idan sama ta tsãge.
2. Kuma idan taurãri suka wãtse.
3. Kuma idan tẽkuna aka facce su.
4. Kuma idan kaburbura aka tõne su.
5. Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
6. Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
7. Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
8. A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
9. A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
10. Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
11. Mãsu daraja, marubũta.
12. Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
13. Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
14. Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
15. Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
16. Bã zã su faku daga gare ta ba.
17. Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
18. Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
19. Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah ( ɗai ) yake.
Sũratul Muɗaffifĩn
Tana karantar da wajabcin tsare haƙƙõkin mutãne tsakaninsu a cinĩki da wasu mu’ãmalolin zamantakẽwa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
2. Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
3. Kuma idan sun auna musu da zakka ( 1 ) ko da sikẽli, suna ragẽwa
4. Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
5. Domin yini mai girma.
6. Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
( 1 ) Mũdu.