Surah Al-Mutaffifin | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 588
Suratul Al-Mutatfifin from 7 to 34
7. Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
8. Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
9. Wani 1ittãfi ne rubũtacce.
10. Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
11. Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
12. Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
13. Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
14. A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
15. A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
16. Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
17. Sa'an nan a ce: « Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi. »
18. A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?
19. Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
20. Wani littãfi ne rubũtacce.
21. Muƙarrabai ( 1 ) suke halarta shi.
22. Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
23. A kan karagu, suna ta kallo.
24. Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.
25. Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
26. Ƙarshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.
27. Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
28. ( Wato ) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
29. Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance ( a dũniya ) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
30. Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
31. Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
32. Kuma idan sun gan su sai su ce: « Lalle waɗannan ɓatattu ne. »
33. Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
34. To, yau fa ( a Lãhira ] waɗanda suka yi ĩmãni,sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
( 1 ) Malã'iku masu daraja.