Hausa translation of the meaning Page No 592

Quran in Hausa Language - Page no 592 592

Suratul Al-Al'la from 16 to 26


16. Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya. ( 1 )
17. Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
18. Lalle ne, wannan ( 2 ) yanã a cikin littafan farko.
19. Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.
Sũratul Ghãshiya
Tana karantar da yin hujja da abin da ake iya gani da ido dõmin a fahimci abin da ake gani da hankali, gwargwadon tunanin abokin magana.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Lalle ne labãrin ( Ƙiyãma ) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
2. Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
3. Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
4. Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
5. Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
6. Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
7. Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
8. Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
9. Game da aikinsu, masu yarda ne.
10. ( Suna ) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
11. Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
12. A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
13. A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
14. Da kõfuna ar'aje.
15. Da filõli ( 3 ) jẽre,
16. Da katifu shimfiɗe.
17. Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
18. Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
19. Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
20. Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
21. sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
22. Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
23. Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
24. To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
25. Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
26. Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.
( 1 ) Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira.
( 2 ) Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko.
( 3 ) Matãsan kai.