Hausa translation of the meaning Page No 593

Quran in Hausa Language - Page no 593 593

Suratul Al-Fajr from 1 to 23


Sũratul Fajr
Tana karantar da cẽwa girmamawa da ĩmãni da taƙawa take bã da sãmun dũkiya ko kyãwon halitta ko mulki ba.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Inã rantsuwa da alfijiri.
2. Da darũruwa gõma.
3. Da ( adadi na ) cikã da ( na ) mãrã.
4. Da dare idan yana shũɗewa.
5. Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali ( da yake kange shi daga zunubi ) ?
6. Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?
7. Iramawa mãsu sakon ( 1 ) ƙĩrar jiki.
8. Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa ( na dũniya ) .
9. Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi ( 2 ) suka yi gidãje
) ?
10. Da Fir'auna mai turãku.
11. Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?
12. Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.
13. Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.
14. Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.
15. To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: « Ubangijina Ya girmama ni. »
16. Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: « Ubangijina Ya walãkanta ni. »
17. A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!
18. Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga ( tattalin ) abincin matalauci!
19. Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.
20. Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.
21. A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.
22. Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu.
23. Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!
( 1 ) Tsawo mai ma'ana.
( 2 ) Wãdil- ƙura, sunan wuri ne kusa da Madina wajen Syria, wato Sham.