Hausa translation of the meaning Page No 597

Quran in Hausa Language - Page no 597 597

Suratul Al-Tin from 1 to 19


Sũratut Tĩn
Tana karantar da cẽwa duka abin da ya shãfi addini bã ya halaka, sauran abubuwa suna halaka da shuɗewar zãmaninsu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn. ( 1 )
2. Da Dũr Sĩnĩna ( 2 ) .
3. Da wannan gari ( 3 ) amintacce.
4. Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
5. Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
6. Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
7. To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako ( wanda za a yi a bãyan Tãshin Ƙiyãma ) ?
8. Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba? ( 4 )
Sũratul ‘Alaƙ
Tana karantar da cẽwa karãtu shi ne gaba da kõme, amma a gama shi da sũnan Allah, kuma a yi aiki da shi domin a sãmi kiyãyewar Allah daga dukan maƙiyin addĩni.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
2. Ya hahitta mutum daga gudan jini.
3. Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
4. Wanda Ya sanar ( da mutum ) game da alƙalami.
5. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
6. A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai ( ya ƙi karatu ) .
7. Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
8. Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
9. Shin, kã ga wanda ke hana.
10. Bãwã idan yã yi salla?
11. Ashe, kã gani, idan ( shi bãwan ) ya kasance a kan shiriya?
12. Ko ya yi umurni da taƙawa?
13. Ashe, kã gani, idan ( shi mai hanin ) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
14. Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
15. A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
16. Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
17. Sai ya kirayi ƙungiyarsa.
18. Zã Mu kirayi zabaniyãwa ( mala'iku mãsu girma ) .
19. A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, ( 5 ) kuma ka nemi kusanta ( zuwa ga Ubangijinka ) .
( 1 ) Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'
( 2 ) Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa.
( 3 ) Gari amintacce shi ne Makkah.
( 4 ) Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci.
( 5 ) Wato salla da sauran ibãdodi.