Hausa translation of the meaning Page No 598

Quran in Hausa Language - Page no 598 598

Suratul Al-Qadr from 1 to 7


Sũratul Kadr
Tana karantar da son Allah ga wannan al’umma ta Musulmi da Ya ba su Lailatul Ƙadari dõmin Ya yawaita ladar ayyukansu ko da yake rãyukansu bã su da tsawo kamar na al’ummomin farko.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi ( Alƙur'ãni ) a cikin Lailatul ƙadari ( daren daraja )
2. To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul Ƙadari?
3. Lailatul Ƙadari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.
4. Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni.
5. Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.
Sũratul Bayyina
Tana karantar da hãlãyen kãfirai da mutãnen Littãfi, wãto Yahudu da Nasãra game da Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, a gabanin da bayan bayyanarsa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu.
2. Wani Manzo ( 1 ) daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki.
3. A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja.
4. Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu.
5. Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai.
6. Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai.
7. Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta.
( 1 ) Shi ne Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, dõmin bãbu wanda ya dãce da abin da ke cikin littafansu sai shi.