Surah Al-Kafirun | Surah An-Nasr | Surah Al-Masad | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 603
Suratul Al-Kafirun from 1 to 5
Sũratul Kãfirũn
Tana bayãnin cẽwa ba a sassautawa ga gaskiya game da addini, dõmin nẽman yardar wasu mutãne ko wani mutum.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ka ce: « Ya kũ kãfirai! »
2. « Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba. »
3. « Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba. »
4. « Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba. »
5. « Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake ( 1 ) bautã wa ba. »
6. « Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni. »
Sũratun Naṣr
Tana nũna ƙãrẽwar aikin Annabi na Manzanci kuma tananũna abin da tsõho zai kãma yi idan aikin ƙarfi ya buwãye shi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara.
2. Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, ƙungiya- ƙungiya.
3. To, ka yi tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi ( Ubangijinka ) Ya kasance Mai karɓar tũba ne.
Sũratul Masad
Tana nũna hushin Allah ga maƙiyin Annabi. Kuma ita da sũrorin da suke bãyanta sunã nũna dogẽwar ƙiyayyar kãfirai gaaddini bãyan ƙaurar Annabi, da dõgẽwar addĩni na gaskiya, kuma Allah zai tsare Musulmin ƙwarai daga dukan sharrin mãsu camfe- camfe da mãsu sanya dasĩsa a cikinsa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka.
2. Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra.
3. Zã ya shiga wuta mai hũruwa.
4. Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen ( wuta ) . ( 2 )
5. A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba ( Rãnar Ƙiyãma ) .
( 1 ) Ãya ta 4 da ta 5 sun nũna addinin ƙarya yakan canza amma na gaskiya bã ya canzawa.
( 2 ) Anã fassara shi da mai tsẽgumi, wãtau annamĩmanci; da Lãrabci anã ce wã mai annamĩmanci « mai ɗaukar itacen wuta. »