Hausa translation of the meaning Page No 602

Quran in Hausa Language - Page no 602 602

Suratul Quraish from 1 to 3


Sũratu Ƙuraish
Tana bayyana darajar Ƙuraishawa da taimakon da Allah Yake yi musu. Hae take da surar Gĩwa amma aka raba su da Basmala dõmin a bambanta darajar Hurumin garin Makkah da kuma ta Ƙuraishawa ƙabilar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Sabõda sãbon Ƙuraishawa.
2. Sãbonsu na tafiyar hunturu da ta bazara.
3. Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida ( Ka'abah ) .
4. wanda Ya ciyar da su ( Ya hana su ) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro.
Sũratul Mã‘ũn
Tana bayãnin yadda zã a iya gãne munafuki da halãyensa atsakãnin Musulmi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
2. To, wannan shi ne ke tunkue marãya ( daga haƙƙinsa ) .
3. Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.
4. To, bone yã tabbata ga masallata.
5. Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu.
6. Waɗanda suke yin riya ( ga ayyukansu )
7. Kuma suna hana taimako.
Sũratul Kauthar
Tana nũna darajar Annabi zuwa ga Allah, yadda Yake yi masa kyauta kuma Ya yi masa faa da maƙiyinsa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Lalle ne Mu, Mun yi maka kyauta mai yawa.
2. Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke ( baiko, wato sukar raƙumi ) .
3. Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka.