Hausa translation of the meaning Page No 76

Quran in Hausa Language - Page no 76 76

Suratul Al-Imran from 195 to 200


195. Sabõda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cẽwa, « Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yãƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna ( waɗanda ) ƙoramu ke gudãna daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako. »
196. Kada jujjuyawar waɗanda suka kãfirta a cikin garũruwa ta rũɗe ka.
197. Jin dãɗi ne kaɗan sa'an nan makõmarsu Jahannama ce, kuma tir da shimfiɗa ita!
198. Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa sunã da Gidãjen Aljanna ( waɗabda ) ƙoramu ke gudãna a ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu, a kan, liyãfa daga wurin Allah, kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alhẽri ga barrantattu.
199. Kuma lalle ne daga Mutãnen Littãfi ( 1 ) haƙĩƙa akwai wanda yake yin ĩmãnĩ da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, sunã mãsu tawãlu'i ga Allah, bã su sayen tamani kaɗan da ãyõyin Allah. Waɗannan suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako da yawa ne.
200. Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku yi haƙuri kuma ku yi dauriya, kuma ku yi zaman dãko, kuma ku yi taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara. ( 2 )
( 1 ) A cikin Mutãnen Littãfi akwai mutãnen ƙwarai na kirki waɗanda hãsada ba ta hana su bin gaskiya ba. Sun sifantu da sifõfin kamãla; watau ba dukkansu ne miyagu ba. Akwai na ƙwarai a cikinsu kamar yadda hãli yake a kõwane tãron mutãne.
( 2 ) Haƙuri a kan ibãda da ɗaukar wahalõlin sharĩ'a gabãɗaya gwargwadon ĩkon yi. Dauriya a kan abokan gaba; watau kada maƙiya su fi mũminai haƙuri wajen yãƙi daɗaukar wahalõlinsa. Zaman dãko ga taushẽwar hanyõyin abõkan gaba daga barin shiga ƙasar Musulmi. Bãbu bambanci ga maƙiyi bayyananne da maƙiyi ɓõyayye Maƙiyi ɓõyayye ya fi aibi dõmin kasancewarsa, zai shiga wuta, amma kasancewarsa maƙiyi bayyananne, zai shiga Aljanna. Taƙawa ita ce bin umuruin Allah da kangẽwa daga barin haninSa kamar yadda Ya faɗa. Wannan shĩ ne kan ibãda duka bãyan ĩmãni, dõmin haka ya ce kõ zã ku ci nasara, idan kun riƙe waɗannan abũbuwa da kyãwo.