Surah An-Nisa | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 77
Suratul Al-Nisa from 1 to 6
Sũratun Nisã’
Tana karantar da hanyõyin tsare haƙƙõƙin jama’a, da alãƙõƙin da suke a tsakãnin al’ummar Musulmi kanta ko kuma a tsakaninta da tsakãnin wata al’umma.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da ( sũnan ) , shi, da kuma zumunta ( 1 ) . Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.
2. Kuma ku bai wa marãyu dũkiyõyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau. Kuma kada ku ci dũkiyõyinsu zuwa ga dũkiyõyinku. Lalle shi, yã kasance zunubi ne mai girma.
3. Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, ( 2 ) to, ( akwai yadda zã a yi ) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu- biyu, da uku- uku, da huɗu- huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, ( ku auri ) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba.
4. Kuma ku bai wa mãtã sadãkõkĩnsu da sauƙin bãyarwa. Sa'an nan idan suka yãfe muku wani abu daga gare shi, da dãɗin rai, to, ku ci shi da jin dãɗi da sauƙin haɗiya.
5. Kada ku bai wa wãwãye ( 3 ) dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kunã mãsu tsayuwa ( ga gyãranta ) . Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufãtar da su, kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri.
6. Kuma ku jarraba marãyu, har a lõkacin da suka isa aure. To, idan kun lura da shiriya daga gare su, to, ku mĩƙa musu dũkiyõyinsu. Kada ku cĩ ta da ɓarna, kuma da gaggawa kãfin su girma. Kuma wanda yake wadãtacce, to, ya kãma kãnsa, kuma wanda yake faƙĩri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun mĩƙa musu dũkiyõyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike.
( 1 ) Bin Allah Wanda Ya halitta ku, kira ga tabbatar da tauhidin Ulũhiyya ne da Rubũbiyya. Fitar mutãne daga asali guda, wanda bãbu wani surki a cikinsa yana wajabtar da girman jinsin mutum, kõwane iri ne, kowane launi, kuma kõwace halitta yake ɗauke da ita.Tsõron Allah da tsaronSa a kan mutãne yana wajabtar da tsayãwa a cikin haddõdin sharĩ'arSa. Tsõron zumunta ko rantsuwa da ita yana wajabtar da tausayi da rahama a kan halittar Allah na kusa da na nesa. Hadĩsi ya nũna ba a yin rantsuwa da wanin Allah sabõda haka ma'anar aya itace, 'Ku ji tsõron Allah ku tsare mahaifa da zumunta!'
( 2 ) Asalin marãya shĩ ne yãron da bai balaga ba, kuma ubansa ya mutu. Amma a cikin ãya- Allah Yã sani- anã nufin dukkan mai rauni a cikin al'umma, wanda yake nẽman a tsare haƙƙin sa da Allah Ya ɗõra wa Musulmi su tsare. Sabõda haka Ya shãfe jawãbin sharaɗin kuma Ya fãra da hukunce- hukunce, a kan tafsĩlin yadda zã a tsare mãsu rauni a cikin al'umma. Ya fãra da mãta a wajen aure, adadinsu daga ɗaya zuwa huɗu, gwargwadon ƙarfin mutum da iyãwarsa ga tsaida ãdalci a gare su, kõ a tsakãninsu. Ãdalci na kwãna da ciyarwa da tufãtarwa.
( 3 ) Sa'an nan yadda ake riƙon dũkiyar wãwã wanda bai san yadda ake riƙon dũkiya ba, ko dã shĩ bãligi ne, yã yi aure, kuma ko da shĩ ne yake nẽman dũkiyarsa da kansa; kamar da ijãra. Wannan wata hanyace ta tsaron haƙƙin mãsu rauni.