Hausa translation of the meaning Page No 78

Quran in Hausa Language - Page no 78 78

Suratul Al-Nisa from 7 to 11


7. Maza suna da rabo ( 1 ) daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke.
8. Kuma idan ma'abũta zumunta da marãyu da matalauta suka halarci rabon, to, ku azurta su daga gare shi, kuma ku faɗa musu magana sananniya ta alhẽri.
9. Kuma waɗanda suke dã sun bar ( 2 ) zuriyya mãsu rauni a bãyansu, zã su ji tsõro a kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana madaidaiciya.
10. Lalle ne, waɗanda suke cĩn dũkiyar marãyu da zãlunci, to, wuta kawai suke ci a cikin cikkunansu, kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani.
11. Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da rabon mãtã biyu. Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce ( kawai ) to, tana da rabi. Kuma iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi ba, kuma iyãyensa ne ( kawai ) suka gãje shi, to, uwa tanã da sulusi ( ɗaya daga cikin kashi uku ) . Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana da sudusi ( ɗaya daga cikin kashi shida ) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa bãshi. Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima.
( 1 ) Hukunce- hukuncen rabon gãdo, hanya ce ta tsaron haƙƙin mãsu rauni.
( 2 ) Watau yadda mutum mai ƙanãnan 'ya'ya yake tsõron ya mutu ya bar su bãbu wata dũkiya da zã ta taimake su, haka kuma su Musulmi waɗanda aka sanya aikin rabon gãdo a hannunsu, su yi tunani, dã su ne suka mutu suka bar 'ya'yansu haka. Sabõda haka wannan zai karya zũciyar mai son ya yi zãlunci daga dũkiyar marãyu.