Surah An-Nisa | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 90
Suratul Al-Nisa from 75 to 79
75. Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã ku yin yãƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka raunanar daga maza da mata da yãra sunã cewa: « Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga wannan alƙarya wadda mutãnenta suke da zãlunci, kuma Ka sanya mana majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa. » ?
76. Waɗanda suka yi ĩmãni, sunã yãki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kãfirta sunã yãƙi a cikin hanyar Ɗãgũtu ( Shaiɗan ) . To, ku yãƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle ne kaidin Shaiɗan yã kasance mai rauni.
77. Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: « Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka. » ? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: « Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa? » Ka ce: « Jin dãɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno! »
78. « Inda duk kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku, kuma kõ da kun kasance ne a cikin gãnuwõyi ingãtattu! » Kuma idan wani alhẽri ya sãme su sai su ce: « Wannan daga wurin Allah ne, » kuma idan wata cũta ta sãme su, sai su ce: « Wannan daga gare ka ne. » Ka ce: « Dukkansu daga Allah ne. » To, me ya sãmi waɗannan mutãne, bã su kusantar fahimtar magana?
79. Abin da ya sãme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutãne, ( kana ) Manzo, kuma Allah Yã isa ga zama shaida.