Hausa translation of the meaning Page No 124

Quran in Hausa Language - Page no 124 124

Suratul Al-Ma'idah from 96 to 103


96. An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dõmin jin dãɗi a gare ku, kuma dõmin matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama mãsu harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tãra ku.
97. Allah Ya sanya Ka'aba Ɗaki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane, kuma Yã sanya watã Mai alfarma da hadaya da rãtayõyin Allah Yã san abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma cewa lalle Allah, ga dukkan, kõme, Masani ( 1 ) ne.
98. Ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne, kuma lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
99. Bãbu abin da yake a kan Manzo, sai iyarwa, kuma Allah Yanã sanin abin da kuke bayyanãwa da abin da kuke ɓõyewa.
100. Ka ce: « Mummuna da mai kyau bã su daidaita, kuma kõ dã yawan mummuan yã bã ka sha'awa. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abuta hankula ko la'alla zã ku ci nasara. »
101. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku ( hukuncinsu ) su ɓãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lõkacin ( 2 ) da ake saukar da Alƙur'ãni, zã a bayyana maku. Allah Yã yãfe laifi daga gare su, Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.
102. Lalle ne wasu mutãne sun tambaye su daga gabãninku, sa'an nan kuma suka wãyi gari da su sanã kãfirai.
103. Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka sã'iba, kuma haka wasĩla, kuma haka hãmi, ( 3 ) amma waɗanda suka kãfirta, su suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma mafi yawansu bã su hankalta.
( 1 ) Dõmin ku san haka kuma ku himmatu ga tsare alkawurranSa.
( 2 ) Wannan lõkacin yã nuna shiɗai ne lõkacin saukar hukunci kõwane iri ne daga Allah. Wanda ya ce Annabi yã faɗa masa wani hukunci a kan wata mastala, bãyan rasuwarsa, tsĩra da aminci su tabbata gare shi, to, bã zã a karɓar masa ba, dõmin yã sãɓã wa nassin Alƙur'ãni. Kuma mafarki bã ya zama hujja, balle a ɗauke shi hukunci wanda ake yin aiki da shi. Mafarkin Annabãwa ko mafarkin da Annabãwa suka tabbatar shi ne gaskiya, saura kuma sai abin da ya bayyana, kuma bai sãɓã wa sharĩa ba.
( 3 ) Bahĩra da sã'iba da hãmi sunãyen dabbõbi ne waɗanda ake bari dõmin tsãfi Bukhãri yã ruwaito daga Sa'ĩd ɗan Musayyab Ya ce: « Bahĩra ita ce rãƙumar da ake hana nõnõnta dõmin aljannu, bãbu mai tãtsar ta daga mutãne. Sã'iba kuma sunã 'yanta ta dõmin gumãka, ba a ɗaukar kõme a kanta. Kuma wasĩla ita ce rãƙuma budurwa wadda ta fãra haifuwar mace, a ciki na farko, sa'an nan kuma na biyu haka mace. Suna barin ta ga gumãka idan ta sãdar da rãƙuma mata biyu bãbu namiji a tsakãninsu. Hãmi kuwa shĩ ne ƙaton rãƙumi wanda ya yi barbara shekaru sanannu a wurinsu. Idan ya ƙãre sai su bar shi ga gumãka, bã a azakõme a kansa. Kuma waɗannan dabbõbin duka, mãsu hidimar gumãkan, su ne suke cin su. »