Hausa translation of the meaning Page No 176

Quran in Hausa Language - Page no 176 176

Suratul Al-A'raf from 196 to 206


196. « Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai, »
197. « Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka. »
198. Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani.
199. Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai. ( 1 )
200. Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani.
201. Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna ( Allah ) sai gã su, sun zama masu basĩra.
202. Kuma 'yan'uwan su ( shaiɗanu ) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bã su taƙaitãwa.
203. Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: « Don me ba ka ƙãga ta ba? » Ka ce: « Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni. »
204. Kuma idan an karanta ( 2 ) Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.
205. Kuma ka ambaci ( 3 ) Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu.
206. Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada.
( 1 ) Baynãnin sifõfin mai wa'azi,watau matminakin gaskiya a kan ƙarya.
( 2 ) Bãyãn an sifanta Alƙur'ãni da cẽwa abin kula ne ga mãsuĩmãni, sai kuma ya yi umurni da saurãre, a lõkacin da ake karatunsa. Sauraren yana wajabta a cikin salla, idan lĩman ya bayyana karãtu kuma da a cikin huɗubar Jumma'a. Yanã zama mustahabbi ga sauran lõkatai. Kur'ãni shi ne abin da ake wa'azi da shi kuma shi ne ãyã da kansa. Hana saurãrensa yãƙi ne da gaskiya.
( 3 ) Sa'an nan kuma ya yi ambaton Allah da addu'a afarko da ƙarshen rãna kamar yadda ya yi umurnida yin salla a waɗannan lõkatai,watau wannan shine makãmin gasikya akan ƙarya.