Surah Al-Anfal | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 186
Suratul Al-Anfal from 70 to 75
70. Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: « Idan Allah Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. »
71. Kuma idan sun yi nufin yaudararka, to, haƙĩƙa, sun yaudari Allahdaga gabãni sai Ya bãyar da dãmã daga gare su: Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
72. Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma ba su yi hijira ( 1 ) ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani.
73. Kuma waɗanda suka kãfirta sãshensu ne waliyyan sãshe, idan ba ku aikata shi ba, wata fitina zã ta kasance a cikin ƙasa, da fasãdi babba.
74. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako, waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani abinci na karimci.
75. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni daga bãya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihãdi tãre da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma'abũta zumunta, sãshensu ne waliyyan ( 2 ) sãshe a cikin Littãfin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kõme Masani.
( 1 ) A farkon Musulunci hijira sharaɗi ce ga shiga cikin waliccin Musulmi, amma bãyan da Musulunci ya yi ƙarfi, hijira ba ta zama sharaɗi ba, sai dai tanã wajaba ga Musulmi ya tashi daga inda bã ya iya tsare addininsa zuwa ga inda yake iya tsare shi, matuƙar bãbu wata wahala mai tsanani. Ana taimakon Musulmin da bai yi hijira ba ga abin da bai shãfi warware alkawarin Musulmi ba.
( 2 ) Walicci shi ne kusanta da lizimtar wajabcin taimakon jũna.A farkon Musulunci, Musulmi bã su da walicci a kan wani Musulmi, sai idan yã yi hijira zuwa Madĩna Bãyan cin Makka da wãtsuwar Musuluncisai waliccin Musulmi ya wajaba a kan kõwane Musulmi a inda duk yake, a cikin dũnlya,gwargwadon hãli, amma kuma a cikin haka mafi kusantar zumuntã shi ne mafi cancanta da waliccin kõwane Musulmi, har dai ga abin da ya shãfi hãlãye na zaman mutum kamar aure da gãdo, da sauransu, kamar yadda littattafan sunna suka bayyana, a can cikin bãbin walicci.