Hausa translation of the meaning Page No 220

Quran in Hausa Language - Page no 220 220

Suratul Yunus from 98 to 106


98. To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi ( 1 ) ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci.
99. Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã waɗanda suke a cikin ƙasa sun yi ĩmãni dukansu gabã ɗaya. Shin, kai kanã tĩlasta mutãnene har su kasance mãsu ĩmãni?
100. Kuma ba ya kasancẽwa ga wani rai ya yi ĩmãni fãce da iznin Allah, kuma ( Allah ) Yanã sanya ƙazanta a kan waɗanda bã su yin hankali.
101. Ka ce: « Ku dũbi abin da yake cikin sammai da ƙasa. » Kuma ãyõyi da gargaɗi bã su wadãtarwa ga mutãne waɗanda bã su yin ĩmãni.
102. To, Shin sunã jiran wani abu fãce kamar misãlin kwãnukan waɗanda suka shũɗe daga gabãninsu? Ka ce: « Ku yi jira! Lalle nĩ tãre da ku, inã daga mãsu jira. »
103. Sa'an nan kuma Munã kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da mãsu ĩmãni.
104. Ka ce: « Yã kũ mutãne! Idan kun kasance a cikin kõkanto daga addinĩna, to bã ni bauta wa,waɗanda kuke, bautã wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rãyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu ĩmãni. »
105. « Kuma ( an ce mini ) : Ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga mãsu shirka. »
106. « Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci. »
( 1 ) Alƙaryun da aka aika da Manzanni cikinsu, ba su yi ĩmãniduka ba fãce mutum ɗaya, kõ biyu a gabãnin halakata sãmi mutãnensu. Sai dai alƙaryar Yũnusa, ita kam tã ji tsõro, ta yi ĩmãni a gabãnin saukar azãba, sabõda haka sukatshĩra, ba a halaka garin bawatau Nĩnawa. Watau bãbu maiiya sãmun ĩmãni sai Allah Ya nufe shi da haka. Kõ da mai yin gargaɗin yakan yiwu ya karkace, sai da tsarin Allah.