Hausa translation of the meaning Page No 235

Quran in Hausa Language - Page no 235 235

Suratul Hud from 118 to 4


118. Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã Yã sanya mutãne al'umma guda. Kuma bã zã su gushe ba sunã mãsu sãɓã wa jũna.
119. Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama, kuma dõmin wannan ( 1 ) ne Ya halicce su. Kuma kalmar « Ubangijinka » Lalle ne zã Ni cika Jahannama da aljannu da mutãne gaba ɗaya « ta cika. »
120. Kuma dũbi dai Munã bã da lãbãri a gare ka daga lãbarun Manzanni, abin da Muke tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan da wa'azi da tunãtarwã ga mãsu ĩmãni.
121. kuma kace wa waɗanda bã su yin ĩmãni, « Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle mũ mãsu aiki ne. »
122. « Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko ( 2 ) ne. »
123. Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake. Kuma zuwa gare Shi ake mayar da dukan al'amari. Sabõda haka ku bauta Masa kuma ku dõgara a kanSa. Kuma Ubangijinka bai zama Mai gafala daga abin da kuke aikatãwa ba.
Sũratu Yũsuf
Tanã karantar da hãlãyen rãyuwar mutum a cikin dũniya tãre da abõkan zama a kõwane matsayi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne.
2. Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta.
3. Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa,daga gafalallu.
4. A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, « Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni. »
( 1 ) Allah ya halicci mutãne da hãlãye dabam- dabam dõmin su sãɓa wa jũna.
( 2 ) Ku yi jira ku gani wãne ne zai ci nasara; mũ da muka bi umurnin Allah, kõ kuwa ku da kuke bin zuciyõyinku. Ãƙiba dai tanã ga mãsu taƙawa. Allah ya tabbatar da mu a kan binsa a kan taƙawa. Amin.