Hausa translation of the meaning Page No 250

Quran in Hausa Language - Page no 250 250

Suratul Al-Ra'd from 6 to 13


6. Kuma sunã nẽman ka da gaggãwa da azãba a gabãnin rahama, alhãli kuwa abũbuwan misãli sun gabãta a gabãninsu. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne ga mutãne a kan zãluncinsu, kuma lalle ne Ubangijinka,haƙĩƙa, Mai tsananin uƙũba ne.
7. Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa don me ba a saukar da wata ãyã a gare shi ba daga Ubangijinsa? Abin sani kawai, kai dai mai gargaɗi ne kuma a cikin kõwaɗanne mutãne akwai mai shiryarwa.
8. Allah Yanã sanin abin da kõwace mace take ɗauke da shi a cikinta da abin da mahaifu suke ragẽwa ( 1 ) da abin da suke ƙãrãwa. Kuma dukkan kõme, a wurinSa, da gwargwado yake.
9. Shi ne Masanin fake da bayyane, Mai girma, Maɗaukaki.
10. Daidai ne daga gare ku, wanda ya asirta magana da wanda ya bayyana game da ita, da wanda yake shi mai nẽman ɓõyewa ne da dare, da mai bayyana a cikin tafiyarsa a hanya da rãna.
11. ( Kowannenku ) Yanã da waɗansu malã'iku mãsu maye wa jũna a gaba gare shi da bãya gare shi, sunã tsare shi daga umurnin Allah. Lalle ne Allah bã Ya canja abin da yake ga, mutãne sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azãba game da mutãne, to, bãbu mai mayar da ita, kuma bã su da wani majiɓinci ( 3 ) baicin Shi.
12. Shĩ ne Wanda Yake nũna muku walƙiya dõmin tsõro da tsammãni, kuma Ya ƙãga halittar girãgizai mãsu nauyi.
13. Kuma arãdu tanã tasbĩhi game da gõde Masa, da malã'iku dõmin tsoronsa. Kuma Yanã aiko tsãwawwaki, sa'an nan Ya sãmi wanda Yake so da su alhãli kuwa sũ, sunã jãyayya a cikin ( al'amarin ) Allah kuma shĩ ne mai tsananin hĩla. ( 4 )
( 1 ) Ragõwar lõkacin cikin ko ƙãruwarsa.
( 2 ) ( 2 ) Hasken rãnã mai kama da ruwa ga idon mai dũbi daga nẽsa.
( 3 ) Bãbu wani majiɓinci baicin Allah, wanda zai iya tsĩrar da su daga azãbarsa.
( 4 ) Hĩla, ita ce mãkirci, Allah Yanã azabta mãsu yin hĩla ga addininsa, da azãba mai tsanani, kuma Ya kãmã su da hĩlarsu ta hanyar da ba su sani ba.