Hausa translation of the meaning Page No 254

Quran in Hausa Language - Page no 254 254

Suratul Al-Ra'd from 35 to 42


35. Misãlin Aljanna wadda aka yi alkawarinta ga mãsu taƙawa, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinta. Abincinta yana madawwami da inuwarta. Waccan ce ãƙibar waɗanda suka yi taƙawa, kuma ãƙibar kãfirai, ita ce wuta,
36. Kuma waɗanda Muka bã su Littãfi sunã farin ciki da abin da aka saukar zuwa gare ka, kuma daga ƙungiyõyi akwai mai musun sãshensa. Ka ce: « Abin sani kawai, an umurce ni da in bauta wa Allah kuma kada in yi shirka da Shi, zuwa gare Shi nake kira, kuma zuwa gare Shi makõmata take. »
37. Kuma kamar wancan ne Muka saukar da shi, ( 1 ) Hukunci a cikin Lãrabci. Kuma lalle ne idan kã bi son zuciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bãbu wani masõyi a gare ka mai kãre ka daga Allah, kuma bãbu matsari.
38. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabãninka, kuma Muka sanya mãtan aure a gare su da zũriyya, kuma ba ya kasancẽwa ga wani Manzo ya zo da wata ãyã, sai da iznin Allah. Ga kõwane ajali ( 2 ) akwai littãfi.
39. Allah Yanã shafe abin da Yake so, kuma Yanã tabbatarwa kuma a wurinsa asalin Littãfin yake.
40. Kuma imma lalle Mu nũna ( 3 ) maka sãshen abin da Muke yi musu wa'adi, kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka to abin sani kawai iyarwa ce a kanka, kuma hisãbi yana gare Mu.
41. Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne, Muna jẽ wa ƙasar ( su ) , Munã rage ta daga gẽfunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shĩ ne Mai gaggãwar sakamako. ( 4 )
42. Kuma lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci. To, ga Allah mãkircin yake gabã ɗaya. Ya san abin da kõwane rai yake tãnada. Kuma kãfirai zã su sani, ga wane ãƙibar gida take.
( 1 ) Kamar yadda littattafan farkosuke, haka Alƙur'ãni yake daga Allah, sai dai shi Alƙur'ãni an saukar da shi a cikin Lãrabci.
( 2 ) Aikõwar Manzanni da littattafai ba ya hana Allah Ya aiko wani Manzo daga bãya da wani littãfi wanda ya shãfe abin da yake cikin littattafan farko. Allah Yã tabbatar da abin da yake so na hukunce- hukuncen da suka gabãta dõmin dõgẽwar aikinsu ga mutãne har yanzu, kuma Ya shãfe abin da yake so sabõda amfãninsu da hukuncinsu yã shige, sabõdawata hikima da Allah Ya sani amma asalin littattãfan duka wanda bã zai canja ba a cikin sanin Allah, yanã wurinsa. « »
( 3 ) Idan Mun so Mu yi musu azãba a gaban idonka zã Mu yi musu, kuma idan Mun so Mu jinkirta musu har a bãyan ka mutu, wannan bã aikinka ba ne, Nãmu ne. Abin da yake aikinka shĩ ne iyar da manzanci kawai. Yin hisãbi a kansu alhakin Allah ɗai ne.
( 4 ) Gaggãwar sakamako ga wanda ya ƙi bin umurnin Allah wanda Annabinsa ya iyar zuwa gare shi. Asalin hisãbi, shine bincike dõmin a sãmi abin da aka yi na alhẽri kõ na sharri amma abin da ake nufi a nan maƙasũdin bincike shĩ ne sakamako da alhẽri kõ da azãba, gwargwadon nufinSa.