Hausa translation of the meaning Page No 255

Quran in Hausa Language - Page no 255 255

Suratul Al-Ra'd from 43 to 5


43. Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: « Ba a aiko ka ba. » Ka ce, « Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da tsakãninku da wanda yake a wurinsa akwai ilmin ( 1 ) Littãfi. »
Sũratu Ibrãhĩm
Tanã karantar da yadda ake yin wa’azi da shiryarwa a game da abin da ya auku ga al’ummõmin da suka shũɗe,na ƙwarai da miyãgu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. R. Littãfi ne mun saukar da shi zuwa gare ka dõmin ka fitar da mutãne daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin Mabuwãyi,Abin gõdẽwa.
2. Allah wanda Yake Yanã da abin da ke cikin sammai da cikin ƙasa. Kuma bone yã tabbata ga kãfirai daga azãba mai tsanani.
3. Waɗanda suka fi son rãyuwar dũniya fiye da ta Lãhira, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah,kuma sunã nẽman ta karkace. Waɗancan na a cikin ɓata mai nĩsa.
4. Kuma ba Mu aika wani Manzo ba fãce da harshen mutãnensa dõmin ya bayyanã musu. Sa'an nan Allah Ya ɓatar da wanda Yake so kuma Ya shiryar da wanda Yake so,Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
5. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Mũsã game, da ãyõin Mu cẽwa, « Ka fitar da mutãnenkadaga duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunar musu da kwãnukan ( masĩfun ) Allah. » Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi dõmin dukan mai yawan haƙuri, mai gõdiya.
( 1 ) Allah Yã isa zama shaida, haka wanda yake a kan wani ilmi daga Allah kamar Yahudu da Nasãra sunã isa zama shaida a tsakãnĩna da ku a kan gaskiyar da'awã ta cẽwa nĩ abin aikõwa ne daga Allah zuwa gardõmin akwai wannan magana a cikin littattafanku.