Surah إبراهيم | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 256
Suratul Ibrahim from 6 to 10
6. Kuma a lõkacin da Mũsã yace wa mutãnensa, « Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da Ya tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã yi muku mummunar azãba, kuma sunã yanyanka ɗiyanku, kuma sunã rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa mai girmã daga Ubangijinku. »
7. Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, « Lalle ne idan kun gõde, haƙĩƙa, Inã ƙãramuku, kuma lalle ne idan kun kãfirta haƙĩƙa azãbãta, tabbas, mai tsanani ce. »
8. Kuma Mũsã ya ce: « Idan kun kãfirta kũ da waɗanda suke a cikin ƙasa, gabã ɗaya, to, lalle ne Allah haƙĩƙa Mawadãci ne, Mai yawan gõdiya. »
9. Shin lãbãrin waɗanda suke a gabãninku, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa bai zomuku ba? Kuma da waɗanda suke daga bãyansu bãbu wanda yake sanin su fãce Allah? Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji mabayyana, sai suka mayar da hannayensu a cikin bãkunansu, kuma suka ce: « Lalle ne mũ, mun kãfirta da abinda aka aiko ku da shi. Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa munã a cikin shakkada abin do kuke kiran mu zuwa gare shi, mai sanya kõkanto. »
10. Manzanninsu suka ce « Ashe, akwai shakka a cikin ( sha'anin ) Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa Yanã kiran ku dõmin Ya gãfarta muku zunubanku, kuma Ya jinkirtã muku zuwa ga ajali ambatacce? » Suka ce: « Ba ku zama ba fãce mutãne misãlinmu kuma nufinku ku kange mu daga abin da iyãyenmu suka kasance sunã bautãwa sai ku zo mana da dalĩli mabayyani. »