Hausa translation of the meaning Page No 265

Quran in Hausa Language - Page no 265 265

Suratul Al-Hijr from 52 to 70


52. A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: « Sallama. » Ya ce: « Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne. »
53. Suka ce: « Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani. »
54. Ya ce: « Shin kun bã ni bushãra ( 1 ) ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara? »
55. Suka ce: « Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni. »
56. Ya ce: « Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu? »
57. Ya ce: « To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni! »
58. Suka ce: « Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi. »
59. « Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ,haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya. »
60. « Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka. »
61. To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,
62. Ya ce: « Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba. »
63. Suka ce: « Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa. »
64. « Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne. »
65. « Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku. »
66. Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba.
67. Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.
68. Ya ce: « Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni. »
69. « Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki. »
70. Suka ce: « Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba? »
( 1 ) Ibrahĩm yanã yi musu tambayã ne dõmin yanã ganin kamar sunã yi masa magana ta izgili ne a kan sãmun ɗã a bãyan tsũfansa da na mãtarsa. Sabõda haka suka gaya masa cẽwa sũ masu gaskiya ne.