Hausa translation of the meaning Page No 266

Quran in Hausa Language - Page no 266 266

Suratul Al-Hijr from 71 to 90


71. Ya ce: « Ga waɗannan, 'ya'yãna ( 1 ) idan kun kasance mãsu aikatãwa ne. »
72. Rantsuwa da ( 2 ) rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
73. Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
74. Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.
75. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.
76. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya. ( 3 )
77. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.
78. Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika ( 4 ) sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
79. Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.
80. Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri ( 5 ) sun ƙaryata Manzanni.
81. Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.
82. Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.
83. Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba.
84. Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.
85. Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a ( Rãnar Alƙiyãma ) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.
86. Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
87. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu ( 6 ) da Alƙur'ãni mai girma.
88. Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i- nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
89. Kuma ka ce: « Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne. »
90. Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa, ( 7 )
( 1 ) Yanã nufin mãtan garin, dõmin Annabin mutãne shĩ ne ubansu.
( 2 ) Allah Yã yi rantsuwã da rãyuwar Annabi Muhammadu, tsĩrã da amincin Allah su tabbata a gare shi. Wannan shĩ ne matuƙar girmamãwr wadda Allah Yake yi wa mutum. Kuma yanã nũna cẽwa rãyuwar Annabi tanã da muhimmanci ƙwarai.
( 3 ) Hanya tabbatacciya ta mutãnen Makka zuwa Syria ( Sham ) .
( 4 ) Ma'abũta Al'aika, sũ ne mutãnen shu'aibu.
( 5 ) Ma'abũta Hijiri, sũ ne samũdãwa.
( 6 ) Bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu su ne Fãtiha mai ãyõyi bakwai. Anã karanta su a cikin kõwace raka'a ta salla.
( 7 ) Mãsu rantsuwa a kan sãɓa wa Annabãwa, watau kamar sun yi rantsuwa cẽwa bã zã su bi abin da Annabãwa suka zoda shi ba. Wãtau su ne mãsu tsananin izgili da addini.