Hausa translation of the meaning Page No 293

Quran in Hausa Language - Page no 293 293

Suratul Al-Asra from 105 to 4


105. Kuma da gaskiya Muka saukar da shi, kuma da gaskiya ya sauka. Kuma ba Mu aike ka ba fãce kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi.
106. Kuma yanã abin karãtu Mun rarraba shi dõmin ka karanta shi ga mutane a kan jinkiri kuma Mun sassaukar da shi sassaukarwa. ( 1 )
107. Ka ce: « Ku yi ĩmãni ( 2 ) da Shi, ko kuwa kada ku yi ĩmãni, lalle ne waɗanda aka bai wa ilmi daga gabãninsa, idan anã karãtunsa a kansu, sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu, sunã mãsu sujada. »
108. « Kuma sunã cẽwa: Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle ne wa'adin Ubangijinmu ya kasance, haƙĩƙa ,abin aikatãwa. »
109. Kuma sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu sunã kũka, kuma yanã ƙara musu tsõro.
110. Ka ce: « Ku kirayi Allah ( 3 ) kõ kuwa ku kirãyi Mai rahama. Kõwane kuka kira to Yanã da sũnãye mafi kyau. Kuma, kada ka bayyana ( 4 ) ga sallarka, kuma kada ka ɓõye ta. Ka nẽmi hanya a tsakãnin wancan. »
111. Kuma ka ce: « Gõdiyã ( 5 ) ta tabbata ga Allah wanda bai riƙi ɗã ba kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa, kuma wani masõyi sabõda wulãkancin bai kasance a gare Shi ba. » Kuma ka girmama Shi, girmamãwa.
Sũratul Kahf
Tanã karantar da ladubban ibãda zuwa ga Allah da yin aiki da zahirin shari’a da barin dukan abin da ya sãɓã wa shari’a.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bãwansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi.
2. Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da ( cẽwa ) sunã da wata lãdã mai kyau.
3. Sunã mãsu zama a cikinta har abada.
4. Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda ( 6 ) suka ce: « Allah yanã da ɗa. »
( 1 ) Saukar da Alƙur'ãni a cikin shẽkaru ashirin ko ashirin da uku ya yi kama da saukar ãyõyin Mũsã tãre a lõkacin da yake kiran Fir'auna zuwa ga addini.
( 2 ) Muƙãranar yin ĩmãni da rashin ĩmãni mutãne ga Alƙur'ãni ba zai rage gaskiyarsa da kõme ba, sai dai waɗanda suka ƙi ĩmãninne zã su cũtu, sa'an nan da bambanci a tsakãnin mai ilmi da jãhili. Mai ilmi yanã da sauƙin jãwuwa zuwa ga gaskiya har ya rasa abin da zai aikata fãce ya fãɗi rikice, a kan haɓarsa, yanã mayrar daal'amari ga Allah kuma yanã tawali'u.
( 3 ) Muƙarana a tsakãnin sũnayen Allah waɗanda ake kiran sa da su wajen rõƙo da waɗanda bã a yin rãko da su. Sũnãyen mafiya kyau da ake kiran Allah da su Hadĩsi ya kãwo su sai a nẽma daga jalãlaini.
( 4 ) Kuma tsakaitãwa wajen karãtun salla ko addu'a kamar yadda aikin Annabi ya nũna yadda ake yi, kada a bayyana kada a ɓõye. Sai dai tsaka.
( 5 ) Ka ce: « Allah ba Shi da abõkin muƙãrna a kõwace jiha. Shi kaɗai Ya cancanci girmamãwa. » Sabõda haka ka girmama Shi, girmãmãwar da ta dãce da Shi.
( 6 ) Lãrabawa sun ce malã'iku 'ya'yan Allah ne. Yahũdawa sunce Uzairu ɗan Allah ne, Nasãra sun ce Ĩsã ɗan Allah ne. Bãbu ladabi ga faɗin wannan magana. Sabõda haka Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya gaya musu, cewa wannan magana ƙarya ce kuma rashin ladabi ne ga Allah, da ba su yi ĩmãni ba, ya ji tsõro kada ya zama shĩ ne ya yi ƙwauron bãki ga faɗã musu gaskiya. Sai Allah Ya gaya masa, cẽwa kada ya halakar da ransa dõmin baƙin cikin haka.