Hausa translation of the meaning Page No 304

Quran in Hausa Language - Page no 304 304

Suratul Al-Kahf from 98 to 110


98. Ya ce: « Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin ( 1 ) Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce. »
99. Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan, yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin ƙaho sai muka tãra su, tãrãwa. ( 2 )
100. Kuma Muka gitta Jahannama, a rãnar nan ga kãfirai gittãwa.
101. Waɗanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunã ( 3 ) Ni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa.
102. Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton ( daidai ne ) su riƙi waɗansu bãyĩNa, ( 4 ) majiɓinta baiciNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai.
103. Ka ce: « Kõ mu gaya muku game da mafĩfita hasãra ga ayyuka? »
104. « Waɗanda aikinsu ya ɓace a cikin rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sunã zaton lalle ne sũ, sunã kyautata, ( abin da suke gani ) aikin ƙwarai? »
105. Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓãci. Sabõda haka bã zã Mu tsayar musu da awo ( 5 ) ba a Rãnar Ƙiyãma.
106. Wancan ne sakamakonsu shĩ ne Jahannama, sabõda kãfircinsu, kuma suka riƙi ãyõyiNa da ManzanniNa abin izgili.
107. Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyãfa a gare su.
108. Suna madawwama a cikinta, bã su nẽman makarkata daga barinta.
109. Ka ce: « Dã tẽku ( 6 ) ta kasance tawada ga ( rubũtun ) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari. »
110. Ka ce: « Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa. » ( 7 )
( 1 ) Wa'adin Ubangiji da fitõwar Yãjũj da Mãjũj. A yanzu bãbu wanda ya san inda suke zaune, sai Allah.
( 2 ) Allah Ya nũna yadda hãlin da zulƙarnaini ya bar Yãjũj da Mãjũj, watau sun garwaya a cikin jũnansu, sa'an nan kuma wannan ma'anar aka bãyar da ita ga mutãne waɗanda ke bin son ransu, bã su bin shari'ar Allah, sunã hargitse a tsakãninsu, har a yi bũsar farko, su mutu, kuma a yi bũsa ta biyu su tãshi a cikin hargitsinsu, sai kuma a gitta Jahannama gaba gare su.
( 3 ) Zikr- tunãwa- shi ne Alƙur'ãni da abin da ya tãra na ibãda da sauran ma'ãmalõli, dukansu ibãda ne, matuƙar an bi abin da Allah Ya ajiye a cikinsu na hukunce- hukunce.
( 4 ) waɗanda suka riƙi wasu bãyin Allah, sunã bauta musu, kamar Yahũdu mãsu bauta wa Uzairu da Nasãra mãsu bautawa Ĩsã da wasu Musulmi mãsu bauta wa wasu sãlihai sun zama kãfirai. Ma'anar bautawar shi ne su ƙirƙira wasu hukunce- hakunce kõ wasu sifõfi waɗanda suka sãɓa wa maganar Alƙur'ãni da Hadĩsi, sa'an nan su jingina su zuwa ga waɗannan bãyin Allah, su bi su da su.
( 5 ) watau ko aunawa bã zã a yi ba balle a daidaita ma'auni.
( 6 ) Ma'anar ãyar nan ita ce Allah ne Mafi sani. llmin Al1ah bã shi da iyãka, kõ kalmõmin da suka ɗauki ma'anõninsa, bã zã a iya rubuta su ba, balle ma'anõnin da ke cikinsu. Sabõda haka abin da ke hankali a mutum, shĩ ne ya yiaiki da ɗan ilmin da Allah Ya umurce shi da aiki dashi. Idan ya nẽmi ya wuce nan, to, ya halakar da kansa dõmin bai san inda zai fãɗa ba. Wannan ilmin shi ne sharĩ'a da aiki da ita.
( 7 ) Wannan ãya, a dunƙule, ta tãra dukan abin da ke cikin sũrar. Allah Ya shiryar da mu, ga kaɗaita shi ga ibãda,da yin ibadar, kuma yadda Allah Ya ce a yĩ ta, ga mai tsammãnin rabo a Lãhira. Wanda ba ya tsammãnin rabon Lãhira, ya tsaya ga dũniya mai gushẽwa da sauri, to, shĩ bã ashiga batunsa ba.