Hausa translation of the meaning Page No 330

Quran in Hausa Language - Page no 330 330

Suratul Al-Anbiya from 91 to 101


91. Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu. ( 1 ) Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.
92. Lalle ne wannan ( 2 ) ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini.
93. Kuma suka kakkãtse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni
94. Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne.
95. Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa.
96. Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa.
97. Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, ( sunã cẽwa ) , « Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci! »
98. ( A ce musu ) « Lalle ne, kũ da abin ( 3 ) da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne. »
99. Dã waɗannan ( abũbuwanbautãwar ) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne.
100. Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme.
101. Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne.
( 1 ) Rũhin Allah a nan, shi ne Malã'ika jibrĩla. Shĩ ne ya hũra a cikin wuyan rĩgarta, sai ta yi cikĩ da Ĩsã. Maryamu bã Annabiya ba ce, an ambace ta ne dõmin shimfiɗa ga maganar Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare Shi. Zamanta ãyã shi ne ta sãmi ɗã bãda namiji ba, kuma wanda ya yi haƙuri ga tsaron haddojin Allah, Allah zai ɗaukaka shi da ni'imar dũniya da ta Lãhira. Ɗanta ya zama ãyã sabõda magana yana yãro, da Annabci da ɗaukar haƙuri ga zartar da umurnin Allah.
( 2 ) Al'ummar Musulmi duka guda ce kõ da yake Annabãwansu sun zo dabam- dabam, a cikin lõkuta mãsu nĩSa tsakãninsu da harsuna dabam- dabam dõmin duk aƙĩdarsu guda ce a kan Ubangiji guda ne. Sa'an nan daga bãya waɗanda suka fita daga wannan aƙĩdar suka rarrabu ƙungiya- ƙungiya.
( 3 ) Bãyin Allah sãlihai da malãiku waɗanda waɗansu mutãne suka bauta musu da tsammãnin cẽwa zã su cẽcẽsu daga Allah, bã zai sanya su Wuta ba sabõda ibãdar da aka yi musu, dõmin yabon Allah yã rigãyi hushinsa zuwa gare su. Bãyansu da mai bautar da wanda ake bautawar kamar gumãka da waɗansunsu, Wuta za su shiga.