Hausa translation of the meaning Page No 331

Quran in Hausa Language - Page no 331 331

Suratul Al-Anbiya from 102 to 112


102. Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa.
103. Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã'iku na yi musu marãba ( sunã cẽwa ) « Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa'adi da shi. »
104. A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon ( 1 ) halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa.
105. Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato ( 2 ) ( Lauhul Mahfũz ) cẽwa ƙasã, bayĩNa sãlihai, sunã gãdonta.
106. Lalle ne a cikin wannan ( Alƙur'ãni ) , haƙĩƙa, akwai iyarwa ( ga maganar da ta gabãta ( 3 ) ga waɗansu mutãne mãsu ibãda.
107. Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai.
108. Ka ce: « Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne? »
109. Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: « Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci? »
110. « Lalle ne Shĩ ( Allah ) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyẽwa. »
111. « Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci. »
112. Ya ce: « Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa. »
( 1 ) Tun da fãrãwa bai buwãye Mu ba mayarwa ba za ta buwãye Mu ba. A Rãnar Ƙiyãma ake naɗe sama kan abin da yake a cikinta kamar yadda ake naɗe takarda a kan abin da ta ƙunsa na rubutun malã'iku a kan bãyin Allah.
( 2 ) Allah Yanã mallakar da ƙasa bãyinsa sãlihai, bã zã ta fita daga gare su ba sai idan sun musanya addininsu na ƙwarai da wani mugu.
( 3 ) Ita ce cẽwar, Allah sãlihai sunã gadon ƙasa.