Hausa translation of the meaning Page No 36

Quran in Hausa Language - Page no 36 36

Suratul Al-Baqarah from 225 to 230


225. Allah ba Ya kãmã ku da laifi sabõda yãsasshiya a cikin rantsuwõyinku. Kuma amma Yana kama ku sabõda abin da zukãtanku ( 1 ) suka sanã'anta. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.
226. Ga waɗanda suke yin rantsuwa ( 2 ) daga matansu akwai jinkirin watã huɗu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
227. Kuma idan sun yi niyyar saki, to, lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.
228. Kuma mãtã waɗanda ( 3 ) aka saki aurensu, suna jinkiri da kansu tsarki uku. Kuma bã ya halatta a gare su, su ɓõye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifunsu, idan sun kasance suna yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma mazan aurensu su ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin gyãrawa. Kuma sũ mãtan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja a kansu ( su mãtan ) . Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
229. Saki sau biyu ( 4 ) yake, sai a riƙa da alh ẽri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku ( maza ) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su ( ma'auran ) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun ( danginsu ) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai.
230. Sa'an nan idan ya sake ta ( na uku ) , to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan ( sãbon mijin, watau na biyu ) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa ( auren ) jũna,idan sun ( mijin farko da matar ) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani.
( 1 ) Yasasshiyar rantsuwa ita ce, a wurin Mãlik, rantsuwa a kan abin da mutum ke ganin satabbatacce ne, sai ya bayyana daga bãya akasin tunãninsa.Kamar ya ce Wallãhi bã ni da kuɗi, ga saninsa kuwahaka ne bã ya da su, bai sani ba ashe wani yã mutu, yã yi gãdo. A shafi'i ita ce: ã'aha Wallahi, I, wallãhi, a cikinmagana bã da nufi ba.
( 2 ) Hukuncin ĩlã'i, watau rantsuwa a kan barin tãkin matarsa dõmin ya wahalar da ita, a jira shi wata hudu, idan yã ƙi kõmãwa a sake ta daga gare shi.
( 3 ) Bayãnin iddar saki da hukunce- hukuncen da suka rãtayu da ita iddar tsarki uku ga mãtar aure ɗiya, baiwa tsarki biyu. Ƙwarƙwara tsarki guda.Istibrã'in zina kõ kuskure kamar idda yake.
( 4 ) Sakin aure da hukunce- hukuncen da suka rãtayu da shi. Wanda ya saki matarsa sau ɗaya ko sau biyu, yanã iya mayar da ita kõ dã ba ta so ba matuƙar ba ta kãre idda ba. Wanda ya yi saki uku, bã ya iya kõma aurenta, sai tã yi jimã'i da wani sãbon miji acikin aure sahĩhi. Sakin bãwabiyu ne.