Hausa translation of the meaning Page No 35

Quran in Hausa Language - Page no 35 35

Suratul Al-Baqarah from 220 to 224


220. A cikin dũniya da Lãhira. Kuma suna tambayar ka game da marãyu. ( 1 ) Ka ce: « Kyautatãwa gare su ne mafi alhẽri, kuma idan kun haɗa da su ( wajen abinci ) , to, 'yan'uwanku ne; kuma Allah Yana sanin mai ɓãtãwa daga mai kyautatãwa. Kuma dã Allah Yã so, dã Ya tsananta muku. Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima. »
221. Kuma kada ku auri mãtã ( 2 ) mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũminaita ce mafi alhẽri daga ɗiya kãfira,kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa.
222. Kuma suna tambayar ka game da haila ( 3 ) Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.
223. Mãtanku gõnaki ne a gare ku, ( 4 ) sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. Kuma ku gabãtar ( da alheri ) sabõda kanku, ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle nekũ mãsu haɗuwa da Shi ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga mũminai.
224. Kuma kada ku sanya ( 5 ) Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.
( 1 ) Bayãnin gama abinci da yãramarãyu mãsu dũkiyar kansu.
( 2 ) Bayãnin irin maza da mãtanwani addini da bã zã a aure su ba sai sun musulunta, watau mushirikai, banda mãtan Mutãnen Littãfi, sũ kam anã auren 'ya'yansu tãre da kãfircinsu. Bã a auren wanda ya yi ridda daga addinin Musulunci.
( 3 ) Bayãnin hukuncin sãduwa damãtan aure a lõkacin hailarsu; watau jima'i ya haramta a cikin haila kõ bãyan haila gabãnin ta yi wanka. Kõ da ta yi taimama tã yi salla duk da haka dai sai tã yi wanka sannan farjinta yake halatta ga mijinta. Amma anã iya mubãshara da rungumayya ko a cikin haila bãyan tã ɗaura gyauto, tã rũfe cĩbiya zuwa gwiwa.
( 4 ) Mutum na iya sãduwa da mãtarsa yadda yake so kuma yadda ya sauƙaƙa a gare shi, daga gaba kõ daga bãya, amma ga farji banda ga dubura. Ma'anar ku gabãtar da alhẽri dõmin rãyukanku, shi ne ku yi basmala ku nẽmi tsari daga Shaiɗan sabõda 'ya'yanku. Ba a jimã'i da mace alhãli tanã barci, ana son gabãtarda wãsa.
( 5 ) Bãyanin rantsuwa da hukunce- hukuncenta. Kada ku sanya rantsuwa da Allah sababin rashin aikata wani alhẽri, kõ wani aikin ɗã'a, kõ kuma sanya sulhu a tsakanin mutãne, kamar a rõƙe shi ga wani abu daga cikinsu, sai ya yi rantsuwa ya ce: « Wallãhi bã zan yi ba, » dõmin tsare kansa daga aikatãwar abin da aka nema gare shi. Yin irin wannanrantsuwa makarũhi ne kõ haram, gwargwadon nauyin abin da aka yi ta sabõda rashin yin sa. Kambu shi ne wurin gwada harbi.