Hausa translation of the meaning Page No 37

Quran in Hausa Language - Page no 37 37

Suratul Al-Baqarah from 231 to 233


231. Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu ( iddarsu ) , sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne.
232. Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu ( iddarsu ) , to, kada ku ( waliyyansu ) hana su, su auri mazansu ( da suka sake su ) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu ( tsõhon miji da tsõhuwar mãta ) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku,kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba.
233. Kuma mãsu haifuwa ( sakakku ) ( 1 ) suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne.
( 1 ) Bayãnin shãyar da mãma ga jinjirin da ubansa ya saki uwarsa a lõkacin shãyarwa ko kuma ta haife shi bãyan sakin yã auku.