Surah Ash-Shu'ara' | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 375
Suratul Al-Shu'ara from 184 to 206
184. « Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko. »
185. Suka ce: « Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne. »
186. « Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata. »
187. « To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya. »
188. Ya ce: « Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa. »
189. Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije ( 1 ) ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.
190. Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
191. Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
192. Kuma lalle shi ( Alƙur'ãni ) , haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne.
193. Rũhi ( 2 ) amintacce ne ya sauka da shi.
194. A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi.
195. Da harshe na Larabci mai bayãni.
196. Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan ( Manzannin ) farko.
197. Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi?
198. Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa,
199. Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba.
200. Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.
201. Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi.
202. Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba.
203. Sai su ce: « Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne? »
204. Ashe, to, da azãbarMu suke nẽman gaggãwa?
205. Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru,
206. Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi ( da shi ) ya jẽ musu,
( 1 ) An ruwaito cẽwa Allah Ya bũɗe musu ƙõfar Jahannama, zãfi ya hana su zama akõ'ina cikin gidãjensu, sa'an nan aka sanya girgije ya yi musu inuwa mai sanyi- sanyi har suka tãru a ciki, sa'an nan aka sanya girgijen ya kãma da wuta a kansu suka ƙõne kurmus kamar an gasa fãra. Suka kõma tõka kamar yadda suka nẽma daga Shu'aibu da a jẽfa musu ɓaɓɓake daga sama idan ya zama daga mãsu gaskiya.
( 2 ) Rũhul Ƙudus, shi ne Jibirĩl, amincin Allah ya tabbata a gare shi.