Hausa translation of the meaning Page No 376

Quran in Hausa Language - Page no 376 376

Suratul Al-Shu'ara from 207 to 227


207. Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare ( 1 ) su.
208. Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi.
209. Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba.
210. Kuma ( Alƙur'ãni ) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba.
211. Kuma bã ya kamãta a gare su ( su Shaiɗãnu su sauka da shi ) , kuma ba su iyãwa.
212. Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne.
213. Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba.
214. Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci.
215. Kuma ka sassauta fikãfikanka ( 2 ) ga wanda ya bĩ ka daga mũminai.
216. Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: « Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa. »
217. Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
218. Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye.
219. Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada.
220. Lalle Shi, ( 3 ) Shi ne Mai ji,Masani.
221. Shin, ( kunã so ) in gaya ( 4 ) muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?
222. Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi.
223. Sunã jẽfa ( abin da suka ) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne.
224. Kuma mawãƙa ( 5 ) halakakku ne ke bin su.
225. Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa ( su ƙẽtare haddi ) ba?
226. Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa?
227. Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa.
( 1 ) Dã an bã su lõkaci mai tsawo sunã jin dãɗi da rãyuwar dũniya a cikinsa, to, rãnar da mutuwa kõ azãbar Allah ta jẽ gare su, wannan lõkacin bã zai tunkuɗe mutuwar kõ azabar ba daga gare su.
( 2 ) Ka zama mai tausayi ga mũminai waɗanda suka bĩ ka, ka yi musu kamar yadda kãzã take yi wa 'ya'yanta ƙanana a lõkacin sanyi, kõ kuwa idan zã su yi barci dõmin ta kãre su daga cũta.
( 3 ) Allah Shi ne Mai ji, ji na gaskiya, kuma Masani, sani na gaskiya.
( 4 ) Wannan dõmin raddi ne gamãsu cẽwa aljannu ke gayawa Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Alƙur'ãni. Aljannu bã su saukã sai ga maƙaryaci, mai zunubi' Muhammadu kuwa bã haka yake ba. Sabõda haka shi bã mahaukaci ba, kuma ba wanda aljannu suke gaya wa ba. Dukan abin da ya faɗa, to, wahayi ne daga Allah.
( 5 ) Siffõfin mawãƙa sun nũna cẽwa Annabi Muhammadu bã mawãƙi ba ne, dõmin bã shi da ɗaya daga cikin siffõfin mawãƙa. Kuma mabiyansa ba halakakku ba ne.