Hausa translation of the meaning Page No 386

Quran in Hausa Language - Page no 386 386

Suratul Al-Qasas from 6 to 13


6. Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su.
7. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi,kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni
8. Sai mutãnen Fir'auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci.
9. Kuma matar ( 1 ) Fir'auna ta ce ( « Ka bar shi yanã ) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, kõ mu riƙe Shi ɗã, » alhãli kuwa sũ ba su sansance ba.
10. Kuma zuciyar uwar Mũsã ta wãyi gari yõfintatta. ( 2 ) Lalle ne, haƙĩƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, bã dõmin Mun ɗaure zũciyarta ba, dõmin ta kasance daga mũminai.
11. Kuma ta ce wa 'yar'uwarsa, ( 3 ) « Ki bĩ shi. » Sabõda haka sai ta lẽƙe shi daga gẽfe, alhãli sũ ba Su sani ba.
12. Kuma Muka hana masa mãsu shãyai da mãma, a gabãnin haka sai ta ce: « Kõ in nũnamuku mutãnen wani gida, su yi muku renonsa alhãli kuwa su mãsu nasĩha ne a, gare shi? »
13. Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa dõmin idanunta su yi sanyi, kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba, kuma dõmin ta san cẽwa lalle wa'adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
( 1 ) Sunan mãtar Fir'auna Ãsiya, tanã da zumunta da Mũsã. Tace ka yi masa sũna 'Mũshã,' ma'anarsa an same shi tsakãnin « mũ, » wãtau ruwa da « shã » watau itãce, sa'an nan ya zama Mũsã. Allah Yanã tsare mutum gaba ga maƙiyinsa.
( 2 ) Zũciya yõfintatta, ita ce wadda bã ta da wani tunãni sabõda abin da ya shagaltar da ita na tunãnin ɗanta a hannun maƙiyinsa.
( 3 ) Sũnan 'yar'uwar Mũsã Maryamu ko Kalsuma ko Kalsumu. Sũnan uwarsu Yũhãniz ɗiyar Hãmid ɗan Lãwaya ɗan Yãƙũbu.