Surah AsSajdah| from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 417
Suratul Al-Sajdah from 21 to 30
21. Kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, mafi ƙasƙanci, kãfin a kai ga azãba mafi girma, dõmin fãtan za su kõmo.
22. Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi.
23. Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littafi, ( 1 ) sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga haɗuwa da shi. Kuma Mun sanya shi ya zama shiriya ga Banĩ Isrã'ĩla.
24. Kuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, sunã shiryarwa da umurninMu, a lõkacin da suka yi haƙuri, kuma sun kasance sunã yin yaƙĩni da ãyõyinMu.
25. Lalle Ubangijinka shĩ ne zai rarrabe a tsakãninsu a Rãnar Ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa.
26. Shin, ba ya shiryar da su cẽwa da yawa Muka halakara gabãninsu, daga al'ummõmi sunã tafiya a cikin masaukansu? ( 2 ) Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi. Shin, ba su jĩ ne?
27. Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle Mũ, Munã kõra ruwa zuwa ga ƙasã ƙeƙasasshiya, sa'an nan Mu fitar, game da shi, wata shũka wadda dabbõbinsu, da su kansu ke ci daga gare ta? Ashe fa ba su gani ba?
28. Kuma sunã cẽwa, « Yaushe wannan hukunci yake, aukuwa idan kun kasance mãsu gaskiya? »
29. Ka ce: « Ranar hukuncin nan, ĩmãnin waɗanda suka kãfirta bã zai amfãne su ba ( a cikinta ) kuma bã zã a yi musu jinkiri ba. »
30. Sabõda haka ka kau da kai daga barinsu, kuma, ka yi jira lalle, sũ ma mãsu jira ne.
( 1 ) Ba Alƙur'ãni ne farkon Littãfin sama ba kuma bã Muhammadu ne farkon Manzannin Allah ba, Mun bai wa Mũsã Attaura, mutãnensa sun yi aiki da ita, sun ɗaukaka kamar yadda ake nẽman Musulmisu yi aiki da Alƙur'ãni su ɗaukaka.
( 2 ) Ƙuraishãwa sunã tafiya a cikin gidãjen al'ummõmin da suka halaka sunã ganin abin daya auku gare su.