Hausa translation of the meaning Page No 443

Quran in Hausa Language - Page no 443 443

Suratul Ya-Sin from 41 to 54


41. Kuma ãyã ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lõdi.
42. Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa.
43. Kuma idan Mun so, zã Mu nutsar da su, har bãbu kururuwar neman ãgaji, a gare su, kuma ba su zama anã tsirar da su ba.
44. Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dãɗi zuwa ga wani ɗan lõkaci.
45. Kuma idan aka ce musu, « Ku kãre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a bãyanku, dõmin tsammãninku a ji tausayinku. »
46. Kuma wata ãyã daga ãyõyin Ubangijinsu bã ta zuwa a gare su, sai sun kasance sunã mãsu bijirẽwa daga gare ta.
47. Kuma idan aka ce musu, « Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku, » sai waɗanda suka kãfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmãni, « Ashe, zã mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yanã ciyar da shi? Ba ku zama ba fãce a cikin ɓata bayyananniya. »
48. Kuma sunã cẽwa, « A yaushe wannan wa'adi yake ( aukuwa ) idan kun kasance mãsu gaskiya? »
49. Bã su jiran ( kõme ) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin husũma.
50. Bã zã su iya yin wasiyya ( 1 ) ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba.
51. Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sunã ta gudu.
52. Suka ce: « Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu? » « Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya. »
53. Ba ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a gare Mu.
54. To, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
( 1 ) Mãsu izgili ga addini idan ajali ya je musu bisa ga abke, bã zã a bã su dãmar wasiyya ba ga iyãlansu.