Hausa translation of the meaning Page No 445

Quran in Hausa Language - Page no 445 445

Suratul Ya-Sin from 71 to 83


71. Shin, ba su gani ba ( cẽwa ) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su?
72. Kuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci.
73. Kuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su gõdẽ ba?
74. Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake su.
75. Bã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa ( a cikin wutã ) .
76. Sabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa.
77. Ashe, kuma mutum bai ga ( cẽwa ) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar.
78. Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: « Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu? »
79. Ka ce: « Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne. »
80. « Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi. »
81. « Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne,Mai ilmi. »
82. UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, « Ka kasance, » sai yana kasancewa ( kamar yadda Yake nufi ) .
83. Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.