Hausa translation of the meaning Page No 446

Quran in Hausa Language - Page no 446 446

Suratul Al-Saffat from 1 to 24


Sũratuṣ Ṣãffãt
Tanã karantar da yadda Allah Ya shirya abũbuwan da ke tunkuɗe mãsu ɓarna a cikin halittarSa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Inã rantsuwa da mãsu yin sahu- sahu ( a cikin salla kõ yãƙi ) .
2. Sa'an nan mãsu yin tsãwa ( 1 ) dõmin gargaɗi.
3. Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
4. Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa Ɗaya ne.
5. Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
6. Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
7. Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
8. Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka ( Malã'iku ) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.
9. Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
10. Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
11. Ka tambaye su: « Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta? » Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
12. Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
13. Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
14. Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
15. Kuma su ce, « Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne. »
16. « Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa,ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne? »
17. « Ashe kõ da ubanninmu na farko? »
18. Ka ce: « Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu. »
19. Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
20. Kuma su ce: « Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako. »
21. Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
22. Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
23. Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
24. Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
( 1 ) Mãsu tsãwa, sũ ne Malamai mãsu sãmun ilmin wa'azi dagaAnnabãwa waɗanda ke karãtun abin tunãwa daga Allah Ubangijin sammai da ƙasa, Mai bãyar da haske ga rãnã, Mai haskaka taurari mãsu ƙãwãtar da samã kuma su tsare ta daga shaiɗanu. An siffanta rãnã da Annabãwa, Malamai da taurãri, ilmi da haske da sababin ƙawa da shiryarwa da kõrar mãsu ɓarna.