Hausa translation of the meaning Page No 444

Quran in Hausa Language - Page no 444 444

Suratul Ya-Sin from 55 to 70


55. Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi.
56. Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira.
57. Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo.
58. « Aminci, » da magana, ( 1 ) daga Ubangiji Mai jin ƙai.
59. « Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi! »
60. « Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne? »
61. « Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya. »
62. « Kuma lalle haƙĩƙa, ( Shaiɗan ) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba? »
63. « Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita. »
64. « Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci. »
65. A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
66. Dã Mun so, dã Mun shãfe gani ( 2 ) daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani?
67. Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba.
68. Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta?
69. Ba Mu sanar da shi ( Annabi ) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi ( Annabi ) ba. Shi ( Al- ƙur'ãni ) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne.
70. Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai.
( 1 ) Ana ce musu aminci ya tabbata a gare ku, da magana daga wajen Ubangijinsu Mai rahama, watau ana fada musu haka da magana bã da wata ishãra ba.
( 2 ) Dã Mun so shãfe ganinsu na ido kamar yadda Muka shãfe basĩrarsu ta hankali, dã Mun shãfe shi, sai su zama makãfin idãnu kamar yadda suke makãfin zũci. Sabõda haka ko sun so gani, bã zã su yi ba.