Hausa translation of the meaning Page No 447

Quran in Hausa Language - Page no 447 447

Suratul Al-Saffat from 25 to 51


25. Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
26. Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
27. Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
28. Suka ce: « Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma ( inda muka amince ) . »
29. Suka ce: « Ã'a, ba ku kasance mũminai ba. »
30. « Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka. »
31. « Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne. »
32. « Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu. »
33. To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
34. Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
35. Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: « Bãbu abin bautãwa, fãce Allah, » sai su dõra girman kai.
36. Kuma sunã cẽwa, « Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci? »
37. Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
38. Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
39. Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
40. Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
41. Waɗannan sunã da abinci sananne.
42. 'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
43. A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
44. A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
45. Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
46. Farã mai dãɗi ga mashãyan.
47. A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
48. Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
49. Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
50. Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
51. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: « Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni ( a dũniya ) . »