Hausa translation of the meaning Page No 460

Quran in Hausa Language - Page no 460

Suratul Al-Zumar from 11 to 21


11. Ka ce: « Lalle nĩ, an umurce ni da in bauta wa Allah, inã tsarkake addini a gare Shi. »
12. « Kuma an umurce ni da in kasance farkon mãsu miƙa wuya ( ga umurnin Allah ) . »
13. Ka ce: « Lalle nĩ inã tsõro, idan na sãɓã wa Ubangijĩna, ga azãbar yini mai girma. »
14. Ka ce: « Allah nake bautã wa, inã mai tsarkake addinĩna a gare Shi. »
15. « To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa. » Ka ce: « Lalle mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar Ƙiyãma. To, waccan fa, ita ce hasãra bayyananna. »
16. Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa.
17. Kuma waɗanda suka nĩsanci Shaiɗannu ga bauta musu, kuma suka mai da al'amari ga Allah, sunã da bushãra. To, ka bãyar da bushãra ga bãyiNa.
18. Waɗanda ke sauraren ( 1 ) magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali,
19. Shin fa, wanda kalmar azãba ta wajaba a kansa? Shin fa, kanã iya tsãmar da wanda ke a cikin wutã?
20. Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah. Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa.
21. Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai tunãtarwa ga mãsu hankali ( ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna ) .
( 1 ) Bãyin Allah na ƙwarai sũ ne waɗanda suke saurãren maganar Allah, sa'an nan su yi aiki da abin da yake mai bayyanannar ma'ana daga gare ta, kuma su bar abin da ba su gãne ma'anarsa ba bãyan sun yi ĩmãni da shi cẽwa daga Allah yake, kuma su tsarkake Allah daga abin da ba ya sifantuwa da Shi na sũrõrin hãlittarSa.