Hausa translation of the meaning Page No 493

Quran in Hausa Language - Page no 493 493

Suratul Zukhruf from 48 to 60


48. Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa.
49. Kuma suka ce: « Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne. »
50. To, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu.
51. Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: « Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba? »
52. « Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar? »
53. « To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe? »
54. Sai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
55. Sabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.
56. Sai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe.
57. Kuma a lõkacin da aka buga misãli da Ɗan Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi ( shi misalin ) sunã dãriya da izgili.
58. Kuma suka ce: « Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi ( Ɗan Maryama ) ? » Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli. ( 1 ) Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.
59. Shi ( Ɗan Maryama ) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla.
60. Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa ( 2 )
( 1 ) Wãtau da aka ce gumãka damãsu bauta musu duka abincin wutar Jahannama ne kamar yadda yake a cikin sura ta 21 ãyã ta 98 da 99, sai suka ce sun yarda gumakansu su zama tãre da ɗan Maryama.
( 2 ) Dã Mun so dã Mun sanya ɗiyansu su zama malã'iku, su fi Ĩsa ɗan Maryama zama abin mãmãki ga halitta, sa'an nan su maye muku a cikin ƙasã maimakon ɗiya masu siffõfi irin na jikunkunanku. Zai fi zama abin mãmãki mutum yahaifi malã'ika bisa mace ta haifi ɗã bã da wani namiji yã kusance ta ba.