Hausa translation of the meaning Page No 526

Quran in Hausa Language - Page no 526 526

Suratul Al Najm from 1 to 26


Sũratun Najm
Tanã tsarkake Annabi da Manzancinsa daga kõwane aibi. Tanã tabbatar da Shi daga Allah, sa’an nan tanã ɓãta dukan abin da bã shi ba na addĩnai da al’ãdu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.
2. Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.
3. Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
4. ( Maganarsa ) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.
5. ( Malã'ika ) mai tsananin ƙarfi ( 1 ) ya sanar da shi.
6. Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.
7. Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.
8. Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.
9. Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.
10. Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah ( Muhammadu ) da abin da ya faɗa ( masa ) .
11. Zũciyar ( Annabi ) bata ƙaryata abin da ya gani ba.
12. Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?
13. Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa ( 2 ) .
14. A wurin da magaryar tuƙẽwa take.
15. A inda taken, nan Aljannar makoma take.
16. Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.
17. Ganinsa ( 3 ) bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
18. Lalle, tabbas, ( Annabinku ) ya ga waɗanda suka fi girma ( 4 ) daga ãyõyin Ubangijinsa.
19. Shin, kun ga Lãta da uzza? ( 5 )
20. Da ( wani gunki wai shi ) Manãta, na ukunsu?
21. Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ ( Allah ) kuma da ɗiya mace?
22. Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.
23. Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. ( Kãfirai ) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ( 6 ) ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu ( sai suka bar ta suka kõma wa zaton ) .
24. Ko ( an fai cẽwa ) mutum zai sãmi abin da yake gũri?
25. To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne ( wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure ) .
26. Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni ( da shi ) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.
( 1 ) Wahayin da ke zuwa ga Annabi bãbu ɓata a cikinsa dõmin Jibrilu mai kãwo shi ga Annabi, Malã'ika ne mai ƙarfi ƙwarai, wani Shaiɗãni bã ya iya taron sa dõmin ya musanya wahayin, kuma Annabiya san shi sõsai, kuma idan ya kãwo wahayin, sai ya sauko kusa ƙwarai da Annabi, sa'an nan shi kuma Annabi ba rikitacce ba ne, yanã cikin hankalinsa.
( 2 ) Lamirin Malã'ika Jibrila ne.
( 3 ) Lamirin Malã'ika Jibrila ne.
( 4 ) Watau dai Alƙur'ani ya zo daga Allah ta hanya mafi aminci har ya sadu da mutãne dõmin su yi aiki da abin da ke cikinsa.
( 5 ) Watau kun bar Alƙur'ani kun kõma wa surkullen da kuke haɗãwa game da gumãka su Lãta da Uzza da Manãta. Kuna cẽwa sũ wakĩlan Mala'ikun da kuke bautã wa ne kuma su 'ya'yan Allah mãtã ne. Sunã cẽton ku daga Allah.
( 6 ) Watau Alƙur'ani wanda Mala'ika jibrĩla ya zo wa Annabi da shi. Sun bar shi sun kõma wa tatsũniyõyi da gũrace- gũrace.