Hausa translation of the meaning Page No 535

Quran in Hausa Language - Page no 535 535

Suratul Al-Waqi'ah from 17 to 50


17. Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
18. Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga ( giya ) mai ɓuɓɓuga.
19. Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
20. Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
21. Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
22. Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
23. Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
24. A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
25. Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
26. Sai dai wata magana ( mai dãɗi ) : Salãmun, Salãmun.
27. Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
28. ( Sunã ) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
29. Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
30. Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
31. Da wani ruwa mai gudãna.
32. Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
33. Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
34. Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
35. Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
36. Sa'an nan Muka sanya su budurwai.
37. Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
38. Ga mazõwa dãma.
39. Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
40. Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
41. Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
42. Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
43. Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
44. Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
45. Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
46. Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
47. Kuma sun kasance sunã cẽwa: « Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan? »
48. « Shin, kuma da ubanninmu na farko? »
49. Ka ce: « Lalle mutãnen farko da na ƙarshe. »
50. « Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne. »