Hausa translation of the meaning Page No 561

Quran in Hausa Language - Page no 561 561

Suratul Al-Tahrim from 8 to 12


8. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi ( 1 ) da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, « Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne. »
9. Yã kai Annabi! Ka yãki kãfirai da munãfwkai. Kuma ka tsananta a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce, kuma tir da makoma, ita.
10. Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka kãfirta ( 2 ) : mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu, sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyi biyu daga bãyinMu sãlihai, saisuka yaudare su, sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: « Ku shiga, kũ biyu, wutã tãre da mãsu shiga. »
11. Kuma Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka yi ĩmãni; matar Fir'auna, ( 3 ) sa'ad da ta ce « Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurinKa a cikin Aljanna. Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutãnen nan azzãlumai. »
12. Da Maryama ( 4 ) ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da LittattafanSa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli'u.
( 1 ) Allah Yã yi alkawarin bã zaikunyltar da AnnabinSa ba, haka kuma waɗanda sukayi ĩmãni tãre da shi, watau sahabbansa a Rãnar Kiyãma. Wannan shĩ ne dalĩlin da ya sa Allah Ya tsare Annabi da Sahabbansa daga bauta musu kamar yadda aka bautã wa waɗansu Annabãwa da Sãlihai waɗanda Allah zai tambaye su kõ sũ ne suka yi umurni da a yi musu bautar, sũ kuma su faɗi barrantarsu daga waɗanda suka bauta musu.
( 2 ) Waɗannan misãlai biyu,mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu sanã nũna kusanci ga sãlihai bã ya isa ga addini sai kõwa ya yi abin da Allah Ya yi umurni da shi. Kuma anã kallafa wa mãtã da su kiyãye kyaun zamantakẽwa da mazansu. Kuma anã yi musu azãba sabõda sãɓa wa Allah ga barin haka kamar yadda ake ga mazansu.
( 3 ) Wannan yanã nũna cẽwa kusantar kãfiri bã zai cũci mũminai ba. Sai dai Allah Yã hana aure a tsakãnin Musulma da kãfiri.
( 4 ) Wannan yanã nũna cẽwa rashin aure ga mãtar da ke iya tsare farjinta daga alfãsha kuma ta tsare addininta da taƙawa, bã zai cũce ta ba ga sãmun rahamar Allah a dũniya da lãhira