Hausa translation of the meaning Page No 565

Quran in Hausa Language - Page no 565 565

Suratul Al-Qalam from 16 to 42


16. Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.
17. Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
18. Kuma ( suka yi niyya ) , bã su kõ tõgẽwa.
19. Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, ( ya ƙone ta, ) alhãli sunã barci.
20. Sai ta wãyi gari ( baƙa ƙirin ) kamar dare.
21. Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
22. Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
23. Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye ( sunã cẽwa ) .
24. « Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau! »
25. Kuma suka yi sammako akan ( niyyar ) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
26. Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: « Lalle, mun saki hanya ( mun ɓace ) ! »
27. « Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne. »
28. Mafificinsu ( hankali ) ya ce: « Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah? »
29. Suka ce: « Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai. »
30. Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
31. Suka ce: « Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka. »
32. « Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ ( ba mu yanke ƙauna ba ) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne. »
33. Haka dai azãbar ( 1 ) take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.
34. Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima.
35. Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?
36. Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci ( da haka ) ?
37. Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
38. Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle ( duk ) abin da rãyukanku suka zãɓa?
39. Kõ kunã ( riƙe ) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar Ƙiyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?
40. Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan ( hukuncin ) ?
41. Kõ sunã da abõkan tãrẽwa ( ga wannan ra'ayi ) ? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.
42. Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba.
( 1 ) Irin wannan azãba ce za a yi wa Ƙuraishãwa, dangin Annabi, kamar yadda aka yi wa mãsu gonar lambu, wãto da suka tũba aka musanya musu da abin da ya fi abin da suka sãba sãmu. Wato an gayã wa Annabi ne lõkacin da danginsa suka kangare, suka ƙi shiga Musulunci, aka yi musu azãbar fari, da rashin ruwa shekara bakwai, Allah Ya gaya masa cẽwa, zã su musulunta, alhẽri ya kõma musu. Ya kuwa kõma, kamar yadda Allah Ya yi alkawari.