Hausa translation of the meaning Page No 566

Quran in Hausa Language - Page no 566 566

Suratul Al-Qalam from 43 to 8


43. Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, ( suka ƙi yi ) .
44. Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri ( Alƙur'ãni ) . Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
45. Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne.
46. Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?
47. Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun ( abin da suke faɗã daga gare shi ) ne?
48. Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
49. Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
50. Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
51. Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu ( kallon mãmãki ) , a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, « Lalle ne shi mahaukaci ne! »
52. Shi ( Alƙur'ãni ) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.
Sũratul Hãƙƙa
Tanã bayanin kiran gaskĩya zuwa ga Allah, Shi kaɗai ne ga sifofinSa da ikonSa, bãbu mai tsõma bãki a cikin ikonSa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Kiran gaskiya!
2. Mẽne ne kiran gaskiya?
3. Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?
4. Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
5. To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
6. Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.
7. ( Allah ) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.
8. To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?