Hausa translation of the meaning Page No 570

Quran in Hausa Language - Page no 570 570

Suratul Al-Ma'arji from 40 to 10


40. Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
41. Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
42. Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari ( da ita ) .
43. Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar ( tuta ) , suke yin gaugãwa.
44. Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari ( a kansa. )
Sũratu Nũḥ
Tana karantar da yadda Annabi Nuhu ya yi gargaɗi gamutãnensa har suka kai ga ya yi addu’a, suka halaka.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
2. Ya ce: « Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa. »
3. « Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni. »
4. « Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana ( ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci ) . »
5. Nũhu
) ya ce: « Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini. »
6. « To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu ( daga gare ni ) . »
7. « Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai. »
8. « Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane. »
9. « Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri. »
10. « Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne. »